Isa ga babban shafi
Turkiya

Ministoci uku sun yi murabus a Turkiya

Ministocin gwamnatin kasar Turkiya guda uku sun yi murabus daga aikinsu sanadiyar wata badakalar rashawa da shafi manyan Jami’an gwamnati da ‘yayansu, wanda hakan baraka ce ga gwamnatin Firaminista Tayyip Racep Erdogan.

Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

A yau Laraba ne Ministan Muhalli ya ajiye aikinsa bayan tuni Ministan Tattalin arziki da na cikin gida suka bayyana yin murabus.

Bayan da Ministan Muhalli ya bayyana yin murabus, ya kuma yi kira ga Firaministan kasar Recep Tayyip Erdogan da ya bi sahunsu saboda binciken rashawa da ake yi a wani banki na Gwamnati.

Wannan dai shi ne aka bayyana a matsayin babban kalubale da Erdogan ke fuskanta tsawon shekaru 11 da ya kwashe yana shugabancin Turkiya.

Tuni ministocinsa biyu na Tattalin arziki da Ministan cikin gida suka yi murabus, sa’o’I kalilan bayan Erdogan ya dawo daga Pakistan inda shugaban kasar Abdallah Gul ke cewa akwai yiyuwar Erdogan zai tankade ministocinsa.

Akwai 'Ya'yan ministocin da ake zargi cikin mutane da dama da ake bincike game da zargin karbar cin hanci.

Erdogan dai ya danganta wannan al’amari a matsayin zagon kasa ga ci gaban tattalin arzikin Turkiya, amma masu lura da siyasar kasar na ganin hakan kuma baraka ce ga Jam’iyyarsa da kawayenta kafin gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Maris da kuma zaben shugaban kasa a watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.