Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta jingine tuhumar da ake wa ‘Yan Green Peace

Kasar Rasha ta yi watsi da tuhumar da take wa ‘yan kungiyar kare muhalli ta Green Peace su 30, lamarin da ya kawo karshen takaddamar watanni uku da aka kwashe ana yi. An kama mutanen ne bayan sun yi yunkurin gudanar da wata zanga zangar nuna kyamar gurbata muhallin tekun Arctic da ke Rasha, inda aka cafke su a matsayin masu fashi a kan teku.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Mikhail Metzel/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Daukar wannan matakin sakin ‘yan kungiyar kare muhalli ta Greenpeace na daga cikin shirin afuwa da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin ke yi a kwanan nan.

Kama mutanen a watan Saaaumba ya jawo suka da dama a sassan daban daban na duniya, wanda hakan ya kara sauya kimar kasar Rasha a idon duniya game da zargin rashin mutunta hakkokin bil adama da ake mata.

Jingine tuhumar da ake wa mutanen, wadanda suka kasance ‘yan kasa daban daban ne, ya biyo bayan sanya hannu da aka yi kan wata sabuwar doka da zata ba su damar ficewa daga kasar.

Ko a karshen makon da ya gabata ma Shugaba Putin ya yi wa Mikhail Kodorkovsky afuwa, fitacce attajiri da aka rufe na tsawon shekaru goma, tare da sakin wasu ‘yan kungiyar mawakan nan na Pussy Riot.

Da yawa dai na ganin wadannan matakai na da nasaba da Gasar Olympics da Rashan za ta karbi bakuncinsa a birnin Sochi a shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.