Isa ga babban shafi
Birtaniya

Kotun Birtaniya ta yanke wa Adebolajo da Adebowale hukunci

Kotun Birtaniya ta yankewa Michael Adebolajo hukuncin daurin rai da rai, tare da yanke wa Michael Adebowale hukuncin daurin shekaru 45 a gidan yari bayan kama su da laifin kisan Sojan kasar Lee Rigby a birnin London.

Michael Adebolajo da  Michael Adebolawe wadanda aka yanke wa hukunci akan kisa Sojan Birtaniya Lee Rigby.
Michael Adebolajo da Michael Adebolawe wadanda aka yanke wa hukunci akan kisa Sojan Birtaniya Lee Rigby. REUTERS/Metropolitan Police/Handout via Reuters
Talla

Wata Kotu ce a birnin London ta yankewa Michael Adebolajo, mai shekaru 29 hukuncin daurin rai da rai tare da yanke wa Michael Adebowale, mai shekaru 22 na haihuwa hukuncin daurin shekaru 45.

Kotun ta kama matasan ne da laifin kashe Sojan Birtaniya Lee Rigby a watan Disemban bara wadanda dukkaninsu ‘Yan kasar Birtaniya ne amma ‘Yan asalin Najeriya da suka musulunta.

A lokacin da mai shari’a Nigel Sweeney ya ke bayyana hukuncin akan matasan, nan take ne kuma Adebolajo ya rura Kotun da Kabbara, “Allahu Akbar”. Yayin da kuma Adebowale ya karyata bayani akan an zansa masu tunani zuwa masu tsatstsauran ra’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.