Joe Biden ya isa Kiev domin ziyarar aiki
Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya isa birnin Kiev na kasr Ukraine domin gudanar da ziyarar aiki, ziyarar da ke zuwa ne a daidai lokacin da masu ra’ayin Rasha ke ci gaba da tayar da kayar baya da kuma mamaye manyan cibiyoyin gwamnati a wasu biranen gabashin Ukraine.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa da ta fiyar kuwa, gwamnatin Rasha ta zargi hukumomin birnin Kiev da karya yarjejeniyar da aka cimma a birnin Geneva cikin makon da ya gabata, wadda ta shata yadda za a warware sabanin da ke tsakanin Ukraine da kuma Rasha.
Ko shakka babu dai ana kallon wannan ziyara ta mataimakin shugaban Amurka Mista Biden a matsayin kara jaddada goyon Amurka ga Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu