Isa ga babban shafi
Ukraine

Ukraine ta kira taron hadin kan kasa

An kaddamar da wani zaman sasanta rikicin kasar Ukraine, da kasashen Yammaci ke marawa baya, ba tare an gayyaci magoya ‘Yan tawaye masu kishin Rasha ba, wadanda ake zargi da yunkurin ci gaba da ruruwa wutar rikicin kasar.

Teburin Sulhunta kasa tsakanin shugabannin Ukraine
Teburin Sulhunta kasa tsakanin shugabannin Ukraine AFP
Talla

An fara zaman tattaunawar ne kwana daya bayan da aka kashe wasu dakarun kasar Ukraine su bakwai a wani harin kwantan bauna a gabashin kasar.

Wannan taro shi ne yunkuri na baya baya nan da kasashen Turai ke kokarin kawo karshen rikicin Ukraine.

Taron sasantawar ya hada da jami’an gwamnatin kasar, da ‘yan majalisar dokokin kasar da kuma ‘yan takarar da za su neman mukamai daban daban a zaben da za a yi a wannan wata.

Sai dai taron, bai gayyaci ‘yan tawayen kasar ba, wadanda suka karbe ikon garuruwa da dama a gabashin kasar tare da yin ikrarin sun balle daga Ukraine bayan da aka gudanar da zaben raba gardama a yankunan Donetsk da Lugansk.

Hakan kuma na faruwa ne duk da cewa mahukuntan kasar sun yada da’awar cewa gayyoto dukkan bangarorin da ke takaddama kan teburin sasantawa shi ne mafita ga rikici na Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.