Isa ga babban shafi
Turai

Shugabannin Turai sun amince su dauki matakai

Shugabannin kasashen Turai sun amince su dauki sabbin matakai wajen tafiyar da harakokin Kungiyarsu bayan kammala zaben ‘Yan majalisu da ‘Yan adawa suka samu kujeru.

Shugaban hukumar Turai Herman Van Rompuy
Shugaban hukumar Turai Herman Van Rompuy Reuters/路透社
Talla

Batun zaben shugabannin hukumar Turai shi ne yanzu ke gaban manyan kasashen Nahiyar irin su Faransa da Jamus da kuma Birtaniya bayan 'Yan adawa a manyan kasashen sun samu kujeru a zaben Majalisa da aka gudanar.

Nasarar da 'Yan adawa suka samu a zaben majalisar Turai da aka gudanar, babban kalubale ne ga manyan kasashen nahiyar masu karfin fada aji musamman ma Faransa inda 'Yan Jam'iyyar 'Yan kishin kasa ta Marine Le pen ta samu kujeru 24 a zauren Majalisar Turai

Wannan kuma shi ya nuna wasu mutanen Turai sun gaji da halin da suka shiga musamman matakan tsuke bakin aljihun gwamanati.

Hakan kuma alamu ne da ke nuna za'a samu sauyin tafiyar da harakokin Turai a wannan karon, saboda karo da 'Yan adawar za su yi da manofofin shugabannin kasashen.

Yanzu batun zaben wadanda zasu jagoranci kungiyar ne ke gaban shugabannin na Turai cikin wadanda ake hasashen zasu jagoranci hukumar Turai sun hada da dan Jam'iyar masu ra'ayin rikau Jean-claude Juncker da kuma Martin na gurguzu wadanda dole sai sun samu rinjayen majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.