EU
Italiya ta nemi a sauya yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasashen Turai
Yayin da ake sa ran kasar Italiya zata karbi ragamar shugabancin kungiyar taraiyyar Turai, Prime Ministaer Matteo Renzi ya nemi a sake sabon lale, kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasashen na Turai. Renzi yace hakan ne kawai zai kawo karshen kyamar da wasu mutanen ke nuna wa kungiyar ta EU.Prime Ministan yace kasashen nahiyar Turai na cikin tsaka mai wuya, kuma akwai bukatar samun yardar jama’a, da suka gaji da matsalolin tattalin arzikin da kasashen suka fuskanta a shekarun baya.
Wallafawa ranar: