Isa ga babban shafi
Britaniya

Ficewar Briataniya daga kungiyar EU zai fi wa birnin London alfanu

Wani rahoton da magajin garin birnin Lodon Boris Johnson ya kaddamar, ya nuna cewa ficewa kasar Britaniya daga kungiyar hadin kan kasashen Turai ta EU, zai fi alfanu ga birnin, maimakon ci gaba da zama. A ranar laraba ake sa rai magajin garin zai yi jawabi ga wasu ‘yan kasuwa a birnin, inda kuma ake ganin zai nuna goyon bayan shi ga rahoton.Ana sa rai in jam’iyyar Prim Minista David Cameron ta lashe zabe a kasar, za a sake duba dangantakar Britaniya da EU, kuma a shekarar 2017 za a yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a don duba yiwuwar kasancewa cikin kungiyar. 

Magajin garin birnin London Boris Johnson
Magajin garin birnin London Boris Johnson REUTERS/Toby Melville
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.