Isa ga babban shafi
Faransa

Shekaru 70 da sojin Afirka suka taimaka don 'yantar da Fransa

A wannan juma’a, shugaba Francois Hollande na Fransa, ya jagoranci wasu bukukuwa da aka shirya domin jinjina wa sojojin kasashen Afirka wadanda suka taimaka domin kwato Faransa daga mamayar kasar Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.

Girmama sojojin Afirka da suka shiga yakin duniya na biyu
Girmama sojojin Afirka da suka shiga yakin duniya na biyu
Talla

Shugaban na Faransa wanda ke gabatar da jawabi a Mont-Faron da ke yankin Toulon, ya bayyana cewa gudunmuwar da sojojin na Afirka suka bayar domin ‘yanto a kasar na a matsayin dalilin samun dankon zumuncin da ba ya tsinkewa tsakanin Afirka da Faransa.

Akwai dai shugabannin kasashen Afirka akalla 15 da suka halarci wadannan bukukuwa na ranar juma’a da aka gudanar a kan wani makeken jirgin ruwan yaki na nukiliya mai suna Charles de Gaulle.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.