Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa tayi bukin samun 'yancin kai

A jiya lahadi ne aka gudanar da bikin tunwa da ranar 19 ga watan Agustan shekarar 1944, da jami’an tsaron kasar Faransa suka soma daga tutar kasar a cikin birnin Paris, bayan birnin ya share shekaru 4 a hannun sojan mamaya na ‘yan Nazin Hitler, a lokacin yakin duniya na biyu.Al’ummar kasar Faransa sun bayyana farin cikinsu tare da yabawa da matsayin ranar, da suka ce tana tattare da dibbin tarihi agare suKasar ta Faransa ta share shekaru da dama a cikin hali na bakin ciki sakamakon mamayar, amma kuma a rana irin wannan, jami’an tsaro dubu biyu ne suka yunkura domin sake kwato wannan wuri.An ci gaba da bikin inda Faransawa suka dinga daga tutar kasar Faransa a wurare daban daban acikin kasar, sannan kuma aka busa taken kasar da ke tabbatar da samun nasara. 

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.