Firaministan Ukraine ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta
Firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Rasha ta tsara bayan Putin ya tattauna da Petro Poroshenko da suka amince a tsagaita wuta a gabacin Ukraine da ‘Yan tawaye suka mamaye. Wannan dai baraka ce ta kunno kai kafin taron da shugabanin kungiyar NATO zasu gudanar inda zasu fi mayar da hankali akan rikicin Ukraine.
Wallafawa ranar:
Firaiministan Yatsenyuk ya bayyana cewar kasar Ukraine ba ta yarda da batun na tsagaita buda Wutar da kasar Rasha ta fito da shi ba domin a ganinsu wani sabon salon yaudarar kasashen Turai ne.
Firaministan yace Rasha tana kokarin kawar da hankalin kasashen Turai ne gabanin babban taron kungiyar NATO da ake shirin yi domin daukar matakai akanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu