Isa ga babban shafi
Ukraine

An yi arangama tsakanin yan sanda da masu hankoron kishin kasa a Ukraine

An yi arangama a jiya talata tsakanin ‘yan kishin kasa da kuma ‘yan sandar kasar Ukraine a harabar ginin majalisar dokokin kasar da ke tabbatar da sabon ministan tsaron kasar a kan mukaminsa.

Le président Petro Porochenko, lors d'une conférence de presse à Kiev, le 25 septembre 2014.
Le président Petro Porochenko, lors d'une conférence de presse à Kiev, le 25 septembre 2014. REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Masu tarzomar dai sun jefa bakin wuta a cikin ginin majalisar, da kuma karya wasu muhimman kadarori na majalisar, abinda shugaban kasar Petro Poroshonko ya bayyana shi da cewa zagon kasa ne.

Kasar Ukraine dai bata bukatar irin wadannan tashe tashen hankulla, ganin yadda a halin yanzu dakarunta ke tabka fada a yankin gabashi, da yan aware masu goyon bayan Rasha

Kasashen turai dai na ci gaba da kakabawa kasar Rasha, tankunkuman kariyar tattalin arziki da nufin tilasta mata tsame kanta daga goyawa yan awaren na Ukraine da suke zargin da yi, da kuma cewa ita ce, ta kirkirosu domin cimma muradunta na kokarin fadada kasarta

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.