Ukraine na cikin shirin ko-ta-kwana
Shugaban Kasar Ukraine Petro Poroshenko yace suna girke Karin sojoji a Gabashin kasar da kuma kara yawan makamai don mayar da martini kan duk wani yunkuri da ‘Yan tawayen ke iya yi na tayar da hankali. Poroshenko yace duk da ya ke suna goyan bayan yarjejeniyar da aka kulla a watan Satumba amma ba za su amince da duk wani shiri na tayar da hankali daga ‘yan tawayen ba.
Wallafawa ranar:
Shugaban yace dakaru yanzu haka na shirin ko ta kwana don kare garuruwan Mariupol da Kharkiv.
An shafe watanni Ukraine na fama da rikicin ‘Yan tawaye masu kishin Rasha da ke neman ballewa daga kasar .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu