Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Rasha na shirin sauya tura Bututubn Iskar Gas daga Ukraine zuwa Turkiyya

Babban kamfanin samar da Iskar Gas na kasar Rasha Gazprom, ya gargadi kasashen Turai da su gaggauta komawa kan bututu kasar Turkiya, kafin su katse Iskar Gas da ke bi ta kasar Ukraine, ko kuma su rasa Iskar Gas din da suke samu a bututu kasar Ukraine

irishoilandgas.wordpre...
Talla

Shugaban kamfanin Alexei Miller shi ya bada wannan sanarawa yayyin wata tattaunawa da sabon kwamishinan Hukumar kula da makamashin nukiliya na tarayyar Turai Maros Sefcivic inda yake cewa za su soke Bututun iskar Gas din kasar ta kudanci da ke bi ta kasar Ukraine zuwa kasashen Turai

Ya ce Turkiya ce za ta zama sabuwar Cibiyar raba Iskar Gas din kamfanin. wanda ya kai cubic Metres biliyyan 63 wanda kuma ke bi ta kasar Ukraine ya koma bi ta kasar Turkiya.

Wannan sabon mataki da kasar Rasha ta dauka na zuwa ne a wani lokaci da dangataka tsakanin Rasha da kasashen Turai ke dada tsami, akan rawar da kasar ke takawa a rikici Ukraine, lamarin da ya sa shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tun a watan Disamban shekarar da ta gabata yake cewa za su yanke tura Iskar Gas din, zuwa Turai ta yankin kasar Ukraine.

Yanzu dai kasar Rasha za ta mayar da Turkiya cibiyar raraba Iskar Gas din kasar. Kasar Turkiya dai ita ce ta Biyu a cikin kasashen da ke shigo da Isakar Gas din Russia kasar su bayan kasar germus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.