Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ana ta barin wuta tsakanin ‘yan tawaye da dakaun gwamnatin Ukraine

Rahotanni daga kasar Ukraine na cewar fada tsakanin ‘yan tawaye masu goyon bayan ballewa zuwa kasar Rasha da kuma Dakarun kasar sai dada kamari yake

Un membre de l'armée ukrainienne disposant des munitions dans un tank posté dans la région de Donetsk, le 13 février 2015.
Un membre de l'armée ukrainienne disposant des munitions dans un tank posté dans la région de Donetsk, le 13 février 2015. REUTERS/Alexei Chernyshev
Talla

An ce dai bangarorin biyu na can suna barin Wuta a yankin gabashin kasar ta Ukraine inda ‘yan tawayen suka yi kaka-gida, a yayin da dakarun gwamnatin kuma ke kokarin kwatar yankin daga hannunsu.

Wannan kuwa na faruwa ne duk da sabuwar yarjejeniyar samar da zaman lafiya da kasashen Faransa da Jamus ke jagoranta tsakanin gwamnatin Ukraine da kuma ‘yan tawayen.

Dama dai shugaban kasar Ukraine Petro Poroshinko ya fada cewar da wuya yarjejeniyar ta yi tasiri lura da yadda ‘yan tawayen ke dada harzuka.

Kassahen Turai kuwa sai kara dabawa kasar Rasha Takunkumman karya tattalin arziki suke da manufar tilastata saduda kan bukatunsu dangane da rikicin na kasar Ukraine, amma Rasha bata yi ko gezau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.