Isa ga babban shafi
Birtaniya

An dawo da jami'ar Birtaniya gida bayan ta kamu da Ebola

Gwamnatin birtaniya ta dawo da wata jami’ar kiwon lafiya 'Yar asalin Birtaniya gida, bayan ta kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo, yayinda a yanzu, zata cigaba da kasancewa a asibitin Kasar

REUTERS/Baz Ratner
Talla

Ma’aikatar tsaron kasar ce ta bayyana haka, inda tace, an aika da jirgin sojin sama zuwa kasar ta Saliyo, inda ya dauko matar domin samun kulawa a asibitin Royal Free dake birnin Landan yayinda kawo yanzu, ba’a bayyana hakikanin halin da matar ke ciki yanzu ba.

Matar dai, ta kasance ta uku cikin ‘ Jami’an kiwon lafiya, ‘Yan asalin birtaniya da suka kamu da cutar ta Ebola, yayinda tuni William Pooley da Pauline Caffarkey suka warke daga cutar bayan sun samu kulawa a asibitin Kasar.

Birtaniya dai, ta maida hankali wajan taimakawa Saliyo dangane da cutar Ebola yayinda ta aika da kimanin sojinta 700 tare da ma’aikatan lafiya kasar, dan kawo karshen cutar.

Tun bayan barkewar cutar, Kimanin mutane dubu 9 ne suka rasa rayukansu a kasashen Saliyo, Guinea da Laberiya kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta sanar kenan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.