Ana zaben Majalisar Dokoki a kasar Turkiyya
A wannan lahadi sama da mutane milyan 53 ne ke jefa kuri’unsu a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Turkiyya, zaben da ake kallo a matsayin zakaran gwajin dafi ga shugaba Racep Tayyip Erdogon, kasantuwarsa zaben majalisa na farko da ake gudanarwa tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar Erdogon dai na bukatar kujeru 330 daga cikin 550 domin ci giaba da kasancewa mai rinjaye a cikin zauren majalisar.
To sai dai manazarta al’amurran siyasar kasar ta Turkiyya na ganin cewa ko a wannan karo jam’iyyar AKP ta shugaban za ta iya yin nasara a zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu