Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Juncker ya roki kasashen turai su dauki nauyin bakin haure

A yau juma’a ne Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar turai Jean-Claude Juncker, ya bayyana cewa, wasu kasashe nahiyar, na jan kafa kan shirin da ya gabatar na yin raba daidai kan daukar nauyin bakin hauren a cikin kasashensu .

shugaban gudanarwa na kungiyar tarayyar turai , Jean-Claude Juncker, a Bruxelles, le 19 mars 2015.
shugaban gudanarwa na kungiyar tarayyar turai , Jean-Claude Juncker, a Bruxelles, le 19 mars 2015. AFP PHOTO / JOHN THYS
Talla

Shirin raba dai dai da bakin hauren tsakanin kasashen turai ya kasance a halin yanzu kasashen Italiya da Girka ne kawai ke fama da wahala, sauran kasashen turan sun noke, a yainda Faransa da Jamus da suka bayyana aniyarsu na tallafawa kasashen daukar nauyin bakin hauren, suka gindaya sharrudi.

A wata fira da tashar France cultur Mr Junka ya ce, shirin da ya gabatar bai samu amincewar wasu kasashe na turan ba, domin daukar nauyin yan gudun hijirar dake bukatar kariyar daga kasashen duniya.

Junka yakara da cewa, baiga abin bacin rai ba, idan wasu kasashen na turai sun ki bada goyon baya ga shirin, domin ya saba ganin haka.

Sai dai duk da haka bai bai dace ba, a bar kasashen Italiya Girka, Malte da Spain su ci gaba da dawainiya da bakin hauren su kadai ba.

Majalisar dinkin diniya ta bayyana cewa, tun farkon wannan shekara 2015 kawo yanzu, bakin haure dubu 51 ne suka kutsa kai a nahiyar turai ta tekun Medetraniyan, dubu 30.500 daga cikinsu na zaune a kasar Italiya. A yayinda bakin hauren 1.800 suka hallaka a ruwa a kokarinsu na kutsa kai a turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.