Isa ga babban shafi
Faransa

An fara baje kolin Paris Air Show

An fara bikin baje kolin Jiragen Sama da ake kira Paris Air Show  a Faransa inda manyan kamfanonin kera jiragen Sama na Airbus da Boeing suka fara da kafar dama.Ana sa ran hallartar mutane dubu 315, da kamfanoni 2,260 daga kasashen duniya 47 a wanan bikin.

Baje kolin Jiragen sama da ake kira Paris Air Show a Fillin Jirgin Le Bourget a Paris
Baje kolin Jiragen sama da ake kira Paris Air Show a Fillin Jirgin Le Bourget a Paris REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Bikin baje kolin Jiragen saman, na mako daya, wanda Shugaban Faransa Francois Hollande ya bude, nan take kamfanin Airbus da Kamfanin Boeing suka sanar da cinikin da ya kai na kudin Amurka dala biliyan 20.

Kamfanin kera Jirage na Airbus ya ce kasar Saudiya ta nemi a sayar mata da Jirage 50 kan kudin daya kai dala biliyan 8, ya yin da kamfanin GE Capital Aviation ya nemi Jirage 60, akan dala biliyan sama da 6.

Kazalika kasar Qatar ta sayi Jirage 14 akan kudi dalar Amurka kusan biliyan 5.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi amfani da damar wajen yabawa sashen harkokin sufurin Jiragen sama a kasar, inda ya ce suna taka rawar gani wajen samar da ayyukan yi ga mutane akalla dubu dari 2, da kuma kudaden da suke juyawa da suka kai euro biliyan 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.