Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar dokokin Faransa ta amince da dokar gurbatar yanayi

Majalisar dokokin Faransa, ta amince da wata doka da gwamnatin kasar ta gabatar, domin tunkarar matsalar gurbatar yanayi mai nasaba da yadda ake amfani da makamashi daga nan zuwa shekara ta 2050 idan Allah ya kai mu.

Shugaban Faransa  Francois Hollande  a zauren taron harkokin kasuwa da sauyin yanayi
Shugaban Faransa Francois Hollande a zauren taron harkokin kasuwa da sauyin yanayi AFP/Pool/Philippe Wojazer
Talla

A karkashin wannan doka da ‘yan majalisar kasar suka amince da ita aranar laraba, wutar lantarki da ake samu daga makamashin nukiliya, ba za ta wuce kashi 50 cikin dari a maimakon kashi 75 cikin dari da ake samarwa yanzu haka.

Dokar wadda gwmanati ta gabatar wa majalisar ana sauran watanni shida a gudanar da taron duniya kan yadda za a tunkari matsalar dumamar yanayi a birnin Paris na Faransa, ta kuma tanadi sabbin ka’idoji dangane da nau’o’in man fetur da kuma iskar gaz da za a rika yin amfani da shi a cikin kasar.

To sai dai kafin soma aiwatar da dokar kamar yadda ake bukata, dole ne gwamnatin Faransa ta sake neman izinin majalisar domin kafa wani asusun tara kudade domin cike gibin hasarar da sauye-sauyen za su iya haifar wa tattalin arzikin kasar a cikin shekaru biyar na farko masu zuwa.

Hakazalika akwai sabbin ka’idoji na biyan haraji ga wasu sinadirai da aka tabbatar da cewa suna taimakawa wajen kara gurbatar muhalli a kasar.
Faransa dai ita ce ta biyu a duniya da ta fi kowace kasa dogara da makamashin nukiliya domin samar da wutar lantarki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.