Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya za ta ci gaba da yakar ‘Yan tawayen Kurdawa

Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce za su ci gaba da kai hare haren sama har sai sun murkushe ‘Yan Tawayen Kurdawa har sai sun kakkabe mayakan.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Darren Whiteside
Talla

A lokacin da ya ke jawabi a Ankara, Erdogan ya ce za su ci gaba da kai hare hare har sai ‘yan tawayen sun aje makamansu.

Shugaban ya bukaci ‘Yan Tawayen na PKK su binne makamansu don tabbatar wa al’ummar kasar cewar su ba wata barazana ba ce.

Turkiya dai na fuskantar barazana daga bangaren ‘Yan tawayen Kurdawa da kuma mayakan ISIL da ke da’awar jihadi a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.