Isa ga babban shafi
Ukraine

Ukraine ta kori wasu ‘Yan jaridar kasashen waje

Gwamnatin kasar Ukraine na fuskantar suka da tir da allawadai akan matakin da ta dauka na haramtawa wasu kafofin yada labarai na kasashen waje gudanar da ayyukansu a cikin kasar da ke fama da rikicin ‘Yan tawaye.

Shugaban Ukraine Petro Porochenko
Shugaban Ukraine Petro Porochenko REUTERS/Valentyn Ogirenko/Files
Talla

Kungiyar kare ‘yan jaridu ta duniya Reporters Without Borders ta yi allawaddai da matakin na gwamnatin Ukraine kan haramtawa wasu ‘yan jarida da ke aiki da kafofin yada labarai na kasashen waje gudanar da aikinsu.

Daga cikin ‘yan jaridar da Ukraine ta kora sun hada da wasu ‘Yan jarida guda uku da ke zama a Rasha wadanda kuma ke aiki da babbar kafar yada labaran Birtaniya BBC.

Kungiyar kare ‘yan jaridun tace wannan mataki ne da ya yi karo da ‘yancin samun bayanai.

Kungiyar kare ‘yan jaridu ta New York tace akwai kimanin yan jarida 41 a jerin sunayen wadanda gwamnatin Ukraine ta Petro Poroshenko ta haramta wa gudanar da aikinsu.

Yanzu haka kuma akwai kudirin doka da gwamnatin Ukraine ke son tabbatarwa akan wasu jami’an kasar da kamfanoni da kuma ‘yan jaridu kan mafarin rikicin ballewar yankin Crimea a bara.

Kasashen Turai da ke goyon bayan gwamnatin Ukraine sun bayyana mamakinsu akan matakin.

Shugaban Rasha Vladimir Putin babban wanda Ukraine ke adawa da shi saboda zargin nuna goyon bayan shi ga ‘Yan a ware ya ce wannan matakin abin ki ne da ya sabawa dokokin ‘yancin fadin albarkacin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.