Isa ga babban shafi
Faransa-Syria

Faransa za ta jagoranci taron tattauna rikicin Syria

Faransa ta bayyana cewa a gobe Talata ne za ta jagoranci taron tattauna rikicin Syria tare da dukkanin bangarorin da ke rikici a kasar.Kasashen da aka gayyata a taron da za’a gudanar a birnin Paris sun hada da Saudiya da Turkiya

ta'adi sakamakon rikicin kasar Syria
ta'adi sakamakon rikicin kasar Syria REUTERS/Houssam Abo Dabak
Talla

kasar  Iran da Rasha ba sa cikin kasashen da Faransa ta gayyata a wannan taron kasancewar su masu banbanci ra’ayi a rikicin na Syria.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce a gobe Talata ne Laurent Fabius zai jagoranci taron tattauna rikicin Syria wanda zai kunshi wasu masu ruwa da tsaki a rikicin kasar.

Za’a gudanar da taron ne dai a birnin Paris kuma Faransa ta gayyaci Jamus da Birtaniya da Saudiya da Amurka aminanta domin tattauna yadda za'a shawo kan rikicin kasar ta Syria.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da ya rage rana guda shugabannin kasashen Rasha da Amurka da Turkiya da Saudiyya su gudanar da taro a Vienna ba tare da Faransa ba.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius yace za'a yi taron ne ba tare da babban jami’in diflomasiyar Rasha ba Sergie Lavrov.

An dadde dai manyan kasashen duniya na tattauna kan rikicin Syria amma ba tare da fito da hanyoyin magance rikicin kasar ba da ya lakume rayukan dubban mutane tare da sa miliyoya gujewa gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.