Spain
Mutane 35 sun hallaka a teku tsakanin Spain da Maroko
Jami’an tsaron gabar ruwan kasar Spain sun dakatar da aikin ceto domin gano wasu mutane 35 da suka bata sakamakon nutsewar kwale-kwalen da suke tafiya a cikinsa tsakanin kasar ta Spain da kuma Maroko.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai magana da yawun hukumar tsaron gabar ruwan kasar da farko ta sanar da cewa an ceto mutane 15 da rayukansu, yayin da har yanzu ba a gano wasu 35 ba.
Rahotanni sun ce ‘yan ci-ranin da lamarin ya shafa sun fito ne daga kasashen Cote d’Ivoire, Nigeria, Mali, Guinea da kuma Kamaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu