Isa ga babban shafi
Turkiya

Jam’iyyar Erdogan ta lashe zaben Turkiya

Jam’iyyar AKP mai mulkin kasar Turkiya ta samu nasara a zaben kasar da aka gudanar a ranar Lahadi, nasarar da za ta ba Jam’iyyar damar kafa gwamnati ba tare da hada kai da wata jam’iyya ba.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Murad Sezer
Talla

Jam’iyar AKP da shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan ya kafa ta lashe sama da kashi 49 na kuri’un da aka kada, wanda ya nuna cewar ta samu kujeru 316 daga cikin kujeru 550 da ke Majalisar a Turkiya.

Sakamakon zaben babbar nasara ce ga Erdogan, wanda ke shirin sauya kundin tsarin mulkin kasar don mayar da kasar zuwa tsarin siyasa irin na Amurka.

Shugaban ya ce nasarar da suka samu ya nuna cewar al’ummar kasar suna bukatar ci gaba da kuma hadin kan al’ummar kasar.

Firaminsita Ahmet Davutoglu ya shaidawa dubban mutanen da suka yi gangami a ofishin jam’iyar cewar zai kare hakkokin al’ummar kasar miliyan 78.

A karon farko Jam’iyyar HDP mai goyan bayan Kurdawa ta samu kujeru a Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.