Isa ga babban shafi
Belgium

Harin Paris: Belgium ta tuhumi mutum na 10

Masu shigar da kara na kasar Belgium sun bayyana cewa an cafke mutum na 10 da ake zargi da hannu a hare haren da aka kaddamar a birnin Paris na Faransa tare da hallaka mutane 130. 

Jami'an tsaron Belgium
Jami'an tsaron Belgium REUTERS/Yves Herman
Talla

Hukumomin Belgium sun bayyana cewa an tsare Ayoub B, mai shekaru 22 da haihuwa sakamakon zarginsa da hannu a hare haren na Paris bayan jami’an tsaro sun cafke shi a lokacin da suka kai samame a wani gida da ke Molenbeek kusa da babban birnin Brussels.

Tuni dai aka tuhumi Ayoub akan aikata laifin kisa ta hanyar ta’addanci da kuma hada kai da kungiyar ‘yan ta’adda, sannann ana sa ran zai sake bayyana a gaban kotu nanda kwanaki biyar masu zuwa.

Tun bayan hare haren Paris, jami’an tsaron Belgium suka matsa bincike domin gano ‘yan ta’adda lura da cewa mutane biyu da suka yi kunar bakin wake a Paris mazauna kasar ta Belgium ne.

A bangare guda, Hukumomin Belgium sun soke bikin wasan wuta da aka saba yi a Breussels domin murnar shiga sabuwar shekara ta 2016 saboda barazanar harin ta’addanci.

Hukumomin Faransa suma sun soke irn wannan bikin a birnin Paris, kuma an girke jami'an 'yan sanda da sojoji 11,000 domin tababtar da tsaro.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.