Isa ga babban shafi
Turkiyya

Akwai bukatar karin tallafin Kudi don dawainiyar ‘yan gudun hijra

Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Turkiyya da kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels, Turkiyya ta bukaci karin kudi har euro biliyan 3 daga kungiyar a matsayin tallafi da zai taimaka mata wajen kula da dubban ‘yan gudun hijrar Syria dake kasar

Shugaba Ahmet Davutoglu na Turkiyya a tsakiyar shugabanin kasashen Turai
Shugaba Ahmet Davutoglu na Turkiyya a tsakiyar shugabanin kasashen Turai REUTERS/Yves Herman
Talla

Kungiyar kasashen Turai ta yi alkawarin bai wa Turkiya euro biliyan uku domin taimakawa ‘yan gudun hijirar da ke kasar, a wani mataki na kawo karshen kwarrarsu zuwa Turai.

Bayan halartar taron kan ‘yan gudun hijira tsakanin Turkiya da tarayyar Turai, Shugaban majalisar dokokin kasashen Turai, Martin Schulz ya shaidawa manema labarai cewa, , Turkiya ta bukaci Karin kudi har euro biliyan uku da take so a bata kafin nan da shekarra 2018.

A bangare guda, shugaban Turkiya, Recep Tayyib Erdogan ya caccaki tarayyar Turai kan daukar dogon lokaci kafin biyan kudaden da aka cimma yarjejeniyar bayar da su a baya domin tinkarar matsalar ta kwararrar baki.

Shugaba Erdogan ya ce, yana fatan Firaiministansa Ahmet Davutoglu wanda a yanzu haka ke birnin Bruseels, zai dawo Turkiya da kudin a hannun sa.

Sama da ‘yan gudun hijira miliyan guda ne suka shiga Turai tun farkon shekarar bara kuma akasarinsuu ‘yan kasar Syria ne da yaki ya tilastawa tserewa daga kasar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.