Isa ga babban shafi
Faransa

Ministocin Faransa sun soki cin zarafin mata

Wata kungiya mai kunshe da tsoffin ministoci mata guda 17 a kasar Faransa, ta yi alla-wadai da wariyar da ake nuna wa mata tare da cin zarafin su ta hanyar lalata da su.

Wasu mata a Faransa da ke zanga zangar nuna adawa da cin zarafin mata a birnin Paris
Wasu mata a Faransa da ke zanga zangar nuna adawa da cin zarafin mata a birnin Paris DOMINIQUE FAGET / AFP
Talla

A cikin wata wasika da suka wallafa a wannan Lahadin, Ministocin sun bukaci a cire rigar kariya ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin matan, sannan sun yi alkawarin cewa ba za su sake yin shiru ba akan cin zarafin.

Wannan dai na zuwa ne, shekaru biyar bayan kama tsohon shugaban asusun bayar da lamuni na duniya, Dominique Strauss Khan a birnin New York na Amurka saboda zargin sa da yin lalata da wata mace.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.