Dubban Jama'a suka shiga Zanga-Zangan Faransa
Mutane akalla 100 ‘Yan sandan Faransa suka kama yayin zanga-zangan a birnin Paris inda dubban mutane suka shiga zanga-zangan don adawa da sabon dokan kodago dake shan suka a kasar
Wallafawa ranar:
‘Yan sandan kwantar da tarzoma akalla 2,000 suka ja daga a sassan birnin Paris domin kare zanga-zangan lumana daga kazancewa,a lokacin da aka fara kwana hudu da fara gasan wasannin kwallon kafan cin kofin Turai da ake bugawa yanzu haka.
Zanga-zangan dai bai kazance ba sosai kasancewar masu zanga-zangan kan rika mikawa ‘yan sanda furanni ne mayayin da suke maci.
Ministan harkokin cikin gida Bernard Caseneuve ya bayyana cewa anyi zanga-zangan cikin natsuwa tunda dai ‘Yan sanda basu yi amfani da barkonun tsohuwa ba, kuma babu wanda ya jikkata.
Hukumomin Faransa na cewa mutane akalla dubu 70 suka shiga zanga-zangan a fadin kasar Alhamis din nan, kodashike kungiyar Kodago na cewa mutane dubu 200 suka shiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu