Isa ga babban shafi
Ingila

Za a fadada filin jirgin Heathrow a London

Gwamnatin Brtaniya ta amince ta fadada fillin jiragen sama Heathrow yau talata, bayan daukan tsawon lokaci ana jan-in-ja a kai, tare da tafka muhawara a cikin shekaru da dama.

Filin jirgin Heathrow a kusa da London
Filin jirgin Heathrow a kusa da London REUTERS
Talla

Fadada filin jirage a kudu maso gabshin Ingila ya biyo bayan amincewar ministocin kasar a wurin wani taron kwamitin majalisar zartarwa na kasar .

Filin jirgin sama Heathrow ya yi fice a duniya, yana da muhimmanci ta fuskar kasuwanci, kuma daukan wannan mataki zai bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da aikin yi ga mutane dubu 77 a tsawon shekaru 14.

Matakin amincewa da fada filin jirgin ya sa hannayen jarin Birtaniya da na Turai sun cira sama.

Gwamnatin Birtaniya ta ce matakin amincewa da fadada filin jirgin babban ci gaba ne ga kasar da ke shirin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.