Isa ga babban shafi
Faransa

An murkushe yunkurin harin ta’addanci a Faransa

‘Yan sandan Faransa sun murkushe wani yunkurin harin ta’addanci a kasar, tare da kame mutane 7 da ake zargi da shirya kai harin a Strasbourg da Marseille.

'Yan sandan Faransa sun murkushe yunkurin harin ta'addanci a Strasbourg da Marseille.
'Yan sandan Faransa sun murkushe yunkurin harin ta'addanci a Strasbourg da Marseille. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ministan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve, ya ce wadanda aka cafke sun hada da ‘yan asalin kasar Morocco da Afghanistan da kuma wani Bafaranshe da suke shirin kai munanan hare hare a kasar.

‘Yan sandan dai sun kaddamar da farmaki ne tun a ranar Asabar bayan jami’an jami’an leken asiri sun shafe watanni takwas suna gudanar da bincike.

Har yanzu Faransa na cikin dokar ta-baci da aka kafa tsawon shekara guda, bayan harin da mayakan IS suka kai birnin Paris da ya lakume rayukan mutane 130 a ranar a 13 ga watan Nuwamban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.