Paparoma Francis ya nemi a yi zaman lafiya a Congo
Shugaban darikar Katolika a Duniya Paparoma Francis a yau lahadi ya yi kira na a rungumi zaman lafiya a yankin Kasai na Jamhurriyar Demokradiyar Kongo dake fama da tashe tashen hankula.
Wallafawa ranar:
Paparoman ya yi wannan kiran ne a yayin da yake jawabi ga mabiya addinin Krista a Capri dake arewacin kasar Italiya inda aka fuskanci munmunar girgizar kasa har sau biyu a shekarar 2012.
Paparoma Francis ya shawarci al’ummar duniya da su mayar da hankali wajen rokon Allah don samun zaman lafiya da kuma sauya tunanin wadanda ke tada zaune tsaye.
Mutane akalla dari hudu ne suka mutu a rikice rikice da aka kwashi sama da watanni shida ana yi a yankunan yammancin Kasai da Lomami dake Jamhurriyar Demokradiyar Kongo cikinsu har da kwararrun ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya guda biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu