Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Faransa: Melenchon na ba da mamaki

Dan takarar shugaban kasa a zaben Faransa na 2017 Jean-Luc Melenchon ya fara razana abokan hamayyarsa a kuri’ar jin ra’ayin jama’a, matakin da ke dada nuna babu tabbas ga wanda zai iya lashe zaben na bana.

Dan takarar shugabancin Faransa Jean-Luc Mélenchon
Dan takarar shugabancin Faransa Jean-Luc Mélenchon GUILLAUME SOUVANT / AFP
Talla

Hankalin ‘yan kasuwa da ‘yan takara ya tashi bayan wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a ya nuna Melenchon ya zo a matsayi na hudu tazarar kuri’a guda tsakanin shi Francois Fillon.

Sannan ya sha gaban dan takarar jam’iyya mai mulki ta Socialist Benoit Hamon.

Hakan dai na nuna zaben zai kasance na yan takara guda hudu Marine Le Pen, da Emmanuel Macron da Francois Fillon da kuma Jean-luc Melenchon.

Tauraron Melenchon da ke haskawa a yanzu shi ne ya mamaye jaridun Faransa, inda jaridar Le Figaro ta danganta manufofinsa da marigayi Hugo Chavez tsohon shugaban Venezuela.

Sai dai an dade ana hasashen Le Pen da Macron za su je zagaye na biyu amma sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka fitar na baya bayan nan na nuna Melenchon na wa ‘yan takarar barazana.

Manufofinsa dai na jan hankalin Faransawa musamman alkawullansa na karfafa haraji ga masu hannu da shuni da barazanar yanke wasu yarjejeniyoyin kasuwanci ta Kungiyar Tarayyar Turai.

Melenchon ya sha alwashin tatsar haraji kashi 100 ga duk wanda ke samun kudi sama da euro dubu arba’in tare da kara yawan kudaden da gwamnati ke kashewa a shekaru biyar.

Nasarar da ya ke samu kuma na kara haifar da barazana ga ‘yan kasuwa da saka jari, musammann yiyuwar ficewar Faransa daga Tarayyar Turai.

Melenchon na da manufofi irin na Le Pen musamman kan masana’tun Faransa da karfafa hulda da Rasha amma sun yi hannun riga ga manufar kyamar baki.

Yadda Melenchon ke jan hankali a yanzu a siyasar Faransa, akan haka ne ya sa shugaba Hollande ya yi gargadi ga Faransawa su kaucewa zaben tumun dare. Musamman wadanda ke kamfen da ya danganta suna alkawullan da basu iya cikawa.

Kamfen din zaben dai yanzu ya koma na caccakar manufofin juna tsakanin ‘yan takarar, musamman yadda sauran ‘yan takarar ke caccakar manufofin Melenchon da Le pen da suka yi alkawalin gudanar da kuri’ar raba gardama kan makomar Faransa a Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.