Isa ga babban shafi
Faransa

Masu yawon bude ido sun karu a Faransa

Adadin masu yawan buda ido da suka ziyarci Faransa a watanni shidan farkon shekarar nan ya karu da kashi 10 da digo 2 cikin dari, abin da ake sa ran dorewarsa zuwa wattani shidan karshen shekarar nan a cewar hukumar da ke kula da shige da ficen baki masu yawan buda ido ta kasar CRT.

daruruwan masu yawon bude ido ne ke ziyartar Faransa a kowanne lokaci, lamarin da ke karawa kasar samun kudaden shiga
daruruwan masu yawon bude ido ne ke ziyartar Faransa a kowanne lokaci, lamarin da ke karawa kasar samun kudaden shiga Reuters
Talla

Kwararru a hukumar ta CRT sun ce a watanni shiddan farkon bana an samu zuwan bakin masu buda ido da suka sauka a hotel miliyan 16 sakamakon da ke nuna karuwar sama da kaso 10 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Hukumar ta ce karancin baki masu yawon bude idon a  2016 na da alaka da hare-haren ta'addancin da aka kaddamar a kasar cikin watan Nuwamban 2015, da kuma yaje yajen aiki da zanga zangogin da kungiyoyin kwadago suka sha gudanarwa wani sa’in ma har da tashin hankali, da hotunan abinda ya faru suka zagaya duniya ya haifar da koma baya ga fannin na buda ido a Faransa.

A game da bakin da suka ziyarci tsibiran da ke karkashin kasar kuwa sun kai miliyan 1 da rabi kari idan aka auna da na watanni shidan farkon 2016 da ya samar da kudaden shiga kimanin Yuro miliyan 1 da digo 1.

A game da kudaden da bakin masu buda ido suka shigar a kasar, sun karu da Yuro miliyan 837, cikin bakin kuwa a cewar sanarwar sun kunshi Amurkawa da 'Yan Chana da Japanawa da kuma 'yan Netherlands.

Rahotan ya ci gaba da cewa Fransawa masu buda ido kadai sun samarwa kasar kimanin Yuro miliyan 224.

Hukumar ta CRT ta ce akwai yiwuwar adadin kudaden da bangaren yawon bude idon zai samar a bana ya haura na shekarar 2015 da ake ganin shi ne mafi yawa da aka tara kimanin Yuro biliyan 21.

Wannan lokaci dai ya nuna sake dawowar masu buda ido da karin kaso 14 da digo 9 musaman Amurkawa sama da miliyan guda da kuma 'yan china  kusan dubu 527 dama sauran 'yan yawon bude idon daga mabanbantan kasashe.

A baya dai makwabtan Faransa musamman 'yan birtaniya ne kan gaba daga cikin baki yan Nahiyar Turai da ke zuwa yawon bude ido a Faransar amma a wannan karon masu yawon bude idon sun fito ne daga kasashe daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.