Wani matashi ya kai wa sojin Belgium farmaki
Jami’an sojin kasar Belgium sun bude wuta kan wani mutum a tsakiyar birnin Brussels, a daren jiya Juma’a, bayanda ya afka musu da sara, a guje, rike da wuka, yana Kabbara.
Wallafawa ranar:
Jami’an soji biyu ne suka samu raunuka sakamakon harin, inda daya ya samu rauni a hannu, dayan kuwa a fuska, sai dai raunukan basu yi muni ba.
Matashin mai shekaru 30, wanda dan asalin kasar Somalia ne, ya mutu, jim kadan bayan da aka garzaya da shi asibiti.
A rahoton da suka fitar hukumomin tsaron kasar ta Belgium, sun ce matashin bashi da tarihin wata alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda ko kuma yinkurin hakan, sai dai sun dauki harin a matsayin na ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu