Isa ga babban shafi
China

China za ta tattauna da Korea ta arewa kan Nukiliya

Kasar China ta sanar da cewa tana gab da tattaunawa da takwararta Korea ta arewa kan bukatun kasashen duniya na dakatar da ita daga hada makaman nukiliya.

Shugaban kasar China Xi Jinping.
Shugaban kasar China Xi Jinping. REUTERS/Jason Lee
Talla

Guo Yezhou shugaban jam’iyyar kwamunisanci, yayin taron jam’iyyar karo na 19 da ke gudana a Beijing ya ce yanzu haka suna shirya yadda za su yi wata tattaunawar fahimtar juna tsakaninsu da Korea ta Arewa wanda kuma su ke fatar ya kawo karshen takaddamar da ake yi.

Duk da cewa dai Yezhou ya ki bayyana takamaiman lokacin da tattaunawar za ta gudana amma ya ce suna yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin alaka tsakanin kasashen biyu bata fuskanci tangarda ba.

Ko a Larabar makon nan dai Korea ta arewa ta aikewa China sakon taya murnar zagayowar ranar taron jam’iyyar duk da matakan da Chinan ke dauka kan shirin Makaminta.

Ana saran dai batun Koriyar ya kasance babban lamari da za a tattaina yayin ziyarar da Trump zai kai ga takwaransa Xi Jinping.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.