Isa ga babban shafi
Faransa

Shekaru biyu da kai harin Bataclan a Paris

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tareda rakiyar tsohon Shugaban kasar Francois Hollande sun halarci gangamin yi tuni da mutanen da suka rasa rayukan su a harin ranar 13 ga watan Nuwemba shekarar 2015 a birinin Paris, hari na Bataclan inda mutane 130 suka rasa rayukansu.

Ranar yi addu'o'i ga mutanen da suka rasa rayukan su a harin Bataclan na Paris a ranar 13-11-2015
Ranar yi addu'o'i ga mutanen da suka rasa rayukan su a harin Bataclan na Paris a ranar 13-11-2015 JOEL SAGET / AFP
Talla

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana alhinin sa tareda jaddada cewa Faransa zata yaki ta'addanci, indan aka yi tuni Hukumomin Faransa  a lokacin harin sun bayyana wani matashi a matsayin mutun na uku da ke da hannu a hare haren ta’addancin da kungiyar ISIS ta kai a birnin Paris, inda mutane 130 suka rasa rayukansu.

Foued Mohamed Aggad mai shekaru 23 na da hannu a harin da aka kai a gidan rawa na Bataclan.

Aggad ya tafi kasar Syria tare da dan uwansa da wasu na kusa da shi a karshen shekara ta 2013, kuma jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu daga cikin su bayan sun dawo Faransa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.