Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta girmama Arnaud Beltrame

Hukumomin Faransa a yau laraba sun girmama dan sandan kasar Arnaud Beltrame mutum na hudu da ya rasa ransa sakamakon harin da wani dan bindiga ya kai kan wani katafaren kanti a kudancin Faransa.

Kanal Arnaud Beltrame dan Sandan da ya sadaukar da ransa
Kanal Arnaud Beltrame dan Sandan da ya sadaukar da ransa Bertrand Guay/AFP
Talla

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yaba da jan kokarin Beltrame, Macron ya bayyana shi a matsayin jarumi.

Idan aka yi tuni dan bindigar ya harbe shi tare da caka masa wuka, Beltrame ya mika kansa ne cikin kantin, domin fansar wata Mata da maharin ya yi garkuwa da ita, kafin daga bisani jami’an tsaro su hallaka dan bindigar.

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce Beltrame ya sadaukar da ransa ga kasarsa Faransa, kuma baza’a manta da bajintarsa ba.

Dubban Faransawa ne suka halara a wannan wuri na place des Invalides domin girmama kanal Arnaud Beltrame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.