Isa ga babban shafi
Faransa

Shugabanni a Faransa na kokarin yiwa Al-qur'ani kwaskwarima

Akalla manyan mutane masu kima da suka hada da tsaffin shugabannin a kasar Faransa 300 ne suka rattaba hannu ga wata manufa ta bukatar yiwa alkur’ani kwaskwarima kamar yadda ake yiwa kudurin Doka a Majalisun jihohi dana tarayya kwaskwarima, a wani mataki na kariya ga Yahudawa.

Matakin sauya wasu ayoyi a Qur'anin na da nufin sanya musulmai su rage kyamar da suke nunawa mabiya addinin Yahudanci.
Matakin sauya wasu ayoyi a Qur'anin na da nufin sanya musulmai su rage kyamar da suke nunawa mabiya addinin Yahudanci. REUTERS
Talla

A ganin manyan mutanen na Faransa dai wannan matakin zai taimaka ga sauya tunanin mabiya Addinin Musulunci su daina kyamar Yahudawa.

Mutanen da suka hada da tsoffin shugabanni da tsaffin ‘Yan Majalisu da tsoffin Alkalai da duk wani da ake cewa shi ne, a kasar ta Faransa su 300, sun gabatar da bukatar ta su ne a Majalisa domin amincewa da ita.

Amincewa da wannan bukatar, da kuma sakata ta kasance doka na nufin a fito da wata sabuwar manakisa ta sauya fasalin ayoyin Alkur’ani domin canja tunanin al’ummar musulmi domin rage kishin Addininsu.

Bukatar wadda aka wallafa ta a Jaridun kasar ta Faransa, ta kuma zargi dabi’ar tsananin kishin addini a matsayin mummunar akidar kyamar Yahudawa da matsuwarsu su fice daga yankin na kasar Faransa.

Bayan gabatar da wannan bukatar da tsoffin kwamayen kasar Faransa suka yi, shugabannin Addinin Musulunci a kasar ta Faransa sun yi kememe akan cewar ba zasu yarda hakan ta faru ba.

Musulmin kasar Faransa kuma sun bayyana wannan matakin da ake shirin dauka a matsayin abinda zai kawo babbar matsala a tsakanin al’ummar kasar da aka sani da zaman lafiya.

Daga cikin dalilan da mawallafan wannan bukatar suka bayana dai, akwai batun yadda ake kai wa Yahudawa hare-hare a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.