Isa ga babban shafi
Amurka

Jakadiyar Amurka a zauren MDD ta yi murabus

Jakadiyar Amurka a zauren majalisar dinkin duniya, Nikki Haley, ta ajiye mukaminta, murabus din da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana amincewa da shi.

Jakadiyar Amurka azauren majalisar dinkin duniya Nikki Haley, tare da shugaba Donald Trump.
Jakadiyar Amurka azauren majalisar dinkin duniya Nikki Haley, tare da shugaba Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Yayin da take bayyana jiye aikin nata, Nikki Haley bata yi karin bayani akan dalilan daukar matakin ba, sai dai ta ce yana da muhimmanci mutum ya gane lokacin da ya dace ya, koma gefe domin samun hutu daga irin dawainiyar aikin da ya shafe tsawon lokaci akai.

Nikki Haley dai za ta cigaba da rike mukaminta har zuwa karshen shekarar 2018 kafin, murabus din nata ya soma aiki.

Jakadiya Haley ta kuma musanta zargin da ake yi mata, na cewa ta yi murabus ne domin fafatawa da Donald Trump, wajen neman kujerar shugabancin Amurka a zaben 2020.

Nikki Haley wadda ‘ya ce ga wasu ‘yan asalin kasar India, asalin sunanta shi ne Nimrata Randhawa, kuma kafin rike mukamin jakadancin Amurka a majalisar dinkin duniya, an zabe ta a matsayin gwamnan jihar South Carolina a shekarar 2010.

A shekarar 2016 Haley ta kasance daga cikin wadanda suka kasance kan gaba wajen sukar manufofin Donald Trump akan baki da ke shiga Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.