Isa ga babban shafi
Amurka

Zanga-zanga kan zaluncin 'yan sanda na cigaba da yin karfi a biranen Amurka

A karon farko tun bayan yakin duniya na 2 gwamnatin Amurka ta baiwa dakarun sojanta na musamman da a turance ake kira da ‘National Guard’ umarnin maido da doka a biranen kasar da dubban mutane ke zanga-zanga kan kashe wani bakar fata da wani jami’in dan sanda mai suna Derek Chauvin yayi a birnin Minneapolis dake Minnesota.

Yadda masu bore euka kone motar 'yan sanda a birnin Atlanta dake jihar Georgia a Amurka. 29/5/2020
Yadda masu bore euka kone motar 'yan sanda a birnin Atlanta dake jihar Georgia a Amurka. 29/5/2020 REUTERS/Dustin Chambers
Talla

Yayin sanar da umarnin aikewa da dakarun sojin, gwamnan jihar ta Minnesota Tim Walz yace daukar matakin ya zama dole, la’akari da cewar wasu bata gari sun soma amfani da zanga-zangar kan mutuwar George Floyd wajen tayar da bore da kuma lalata dukiya.

Gwamnan ya ce duba da irin barnar dake aukuwa an baiwa ilahirin dakarun sojin na musamman dubu 13 dake jihar ta Minnesota umarnin daukar matakan kwantar da tashin hankalin dake neman kazanta.

A halin da ake ciki zanga-zangar ta bazu zuwa Washington, New York, Pennsylvania, Chicago, Atlanta, kuma Los Angeles bayaga Minneapolis dake Minnesota inda boren ya soma, wannan tasa zanga-zangar zama cikin mafi muni da Amurka ta gani a shekaru da dama.

Masu zanga-zangar dai na cigaba da yin arrangama da ‘yan sanda a wasu sassan biranen da boren ke gudana, inda Los Angeles sai da jami’an tsaro suka yi amfani da harsasan roba, yayinda a Atlanta gungun matasa suka cinnawa wata motar ‘yan sanda wuta.

A halin da ake ciki gwamnati ta kafa dokar hana fita a biranen da zanga-zanga kan mutuwar bakar fatar a hannun ‘yan sanda ta juye zuwa tarzoma, sai dai duk da haka sabuwar zanga-zanga ta barke a gaf da fadar gwamnatin Amurka ta White House dake birnin Washington.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.