Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan fashi sun yi awon gaba da dala miliyan 10 a birnin Lyon

Jami’an tsaron Faransa sun ce wasu kasurguman ‘yan fashi sun yi awon gaba da tsabar kudi hannu akalla dala miliyan 10, a birnin Lyon.

Birnin Lyon dake kudu maso gabashin Faransa.
Birnin Lyon dake kudu maso gabashin Faransa. AFP
Talla

Shaidun gani da ido sun ce an tafka muguwar satar ce a jiya Juma’a, jim kadan bayan da motar reshen babban bankin Faransa ta fito daga harabarsa a birnin na Lyon.

Bayanai sun ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata yayin fashin miliyoyin dalar, da wasu suka bayyana barayin sun aiwatar tamkar a shirin fina-finai.

Hukumomin tsaron Faransa sun ce satar ta baya bayan nan ita ce mafi muni da aka gani a kasar, tun bayan ta shekarar 2009, da kasurgumin dan fashi Toni Musulin ya jagoranta, inda yayi awon gaba da euro miliyan 11 da dubu 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.