Isa ga babban shafi
Duniya

Isra'ila zata kulla dangantaka da karin kasashe 6 - Trump

Shugabannin Kasashen Bahrain da Daular Larabawa da kuma Israila sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da kuma cigaba da huldar diflomasiya a tsakaninsu, a wajen wani gagarumin taro da shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta a fadarsa.

Ministocin harkokin wajen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Donald Trump da Benjamin Netanyahu a fadar White House, 15 ga Satumba 2020.
Ministocin harkokin wajen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Donald Trump da Benjamin Netanyahu a fadar White House, 15 ga Satumba 2020. REUTERS/Tom Brenner
Talla

Daruruwan baki ne suka halarci bikin sanya hannu a kan yarjejeniyar kulla huldar diflomasiyar da aka yi a Washington, cikin su har da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan harkokin wajen Bahrain Abdallah Bin Zayed al Hayan da takwaran sa na Daular Larabawa.

Kasashen Bahrain da Daular Larabawa ne kasashen Larabawa guda biyu da suka kulla hulda da Israila tun bayan wanda kasar Masar tayi a shekarar 1979 da kuma Jordan a shekarar 1994.

Shugaba Trump ya ce bayan kwashe shekaru da dama ana tashin hankali, an bude sabon babi a Gabas ta Tsakiya inda mazauna yankin suka zabi zaman lafiya maimakon fadace fadace da kuma zabin cigaba maimakon akasin haka.

Shugaban ya ce yarjejeniyar za ta zama ginshikin samun dawamammen zaman lafiya a fadin yankin baki daya, kuma nan gaba kadan za’a samu Karin kasashen da zasu bi sahun Bahrain da Daular Larabawa.

Shugaba Trump yace sun yi kyakyawar tattaunawa da Saudi Arabia kan lamarin, kuma ya fahimci kofar su a bude take.

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana sanya hannun a matsayin wani sabon babin zaman lafiya da zai hada kan ‘yayan Annabi Ibrahim.

Ministan harkokin wajen Daular Larabawa Abdullah bin Zayed al-Nahyan ya godewa Netanyahu wanda yace ya kama hanyar zaman lafiya maimakon cigaba da mamaye yankunan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.