Kasashen Turai za su kafa dokokin yaki da akidun tsattsauran ra'ayi
Ministocin tarayyar Turai sun cimma matsayar tsaurara matakan tsaro kan iyakokin kasashensu, da kuma samar da dokoki masu tsauri na yakar manufofin yada akidar tsattsauran ra’ayi ta kafofin intanet.
Wallafawa ranar:
Taron ministocin Turan da ya gudana a birnin Brussels na zuwa ne bayan jerin hare-haren da masu tsattsauran ra’ayi suka kai a Jamus, Austria da Faransa ciki har da na baya bayan nan.
Ministocin cikin gidan sun bayyana fatan kammala tattaunawa da hukumar gunarwar kungiyar tarayyar Turai EU da kuma majalisar ta kafin karshen wannan shekara, don samar da dokokin yakar yada manufofin tsattsauran ra’ayi ta shafukan intanet.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu