Isa ga babban shafi

Covid -19: Kwararru na kira da a garkame Faransa karo 3

Adadin wadanda cutar coronavirus ta kai su ga kwanciya a asibiti a Faransa ya karu da fiye mjutan dubu daya a cikin kwanaki 2 da suka wuce, wadanda kuma cutar ta aike da su bangaren kula da marasa lafiya da ke halin rai kwakwai – mutu kwakwai ya zarce dubu 3 a karon farko tun daga ranar 9 ga watan Disamban 2019, lamarin da ya sa kwaru ke kira da a garkame kasar akaro na 3.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP News
Talla

Kwararru a fannin lafiya su na wannan yi kiran ne a daidai lokacin da Faransa ke ci gaba da yi  wa al’umarta rigakafin cutar Coronavirus, amma kafafen yada labaran Faransa sun ruwaito cewa shugaba Emmanuel Macron na kokarin kauce wa haka.

Ya zuwa wannan Litinin, Faransa ta yi wa mutane sama miliyan daya allurar rigakafi.

Macron na fatan cewa dokar takaita zirga zirga da ke farawa daga karfe 6 na yamma da aka sanya kwanaki 10 da suka wuce, za ta dakile yaduwar cutar da ta sake kunno kai.

Raguwar adadin wadanda ake yi wa magani a sashen marasa lafiya da ke halin rai kwakwai- mutu kwakwai zuwa kasa da dubu 3 ne ta sa hukumomin Faransa suka maye gurbin dokar garkame kasa, da ta takaita zirga zirga a ranar 15 ga watan Disamban 2020.

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya shaida wa wata kafar talabijin cewa sake garkame kasar zai jefa ta cikin mawuyacin halin tattalin arziki, ya kuma hana ta cimma hasashenta na samun ci gaba a bangaren da kashi 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.