Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na yaki da masu kyamar baki a kasar

Gwamnatin Faransa ta fara aiwatar da shirin rusa wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayi da kuma kyamar baki a kasar, matakin da kungiyoyi da dama da jam'iyyun siyasa suka dade suna bukata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP News
Talla

Ministan Cikin Gidan Faransa Gerald Darmanin ya sanar da daukar wannan mataki ta shafinsa na Twitter tare da bai wa kungiyar da ke kiran kanta Generation Identitaire a turance kwanaki 10 domin ta kare kanta.

Tun a ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata ministan ya ce, aka fara daukar wannan mataki na rushe kungiyar a hukumance, bayan wani kazamin farmaki da ‘ya’yanta suka kai wa baki kan iyakar kasar, wanda tuni wasu masu rajin kare hakkin bil’adama suka shigar da kara, yayin da gwamnati ita ma ta bude bincike.

A ranar 19 ga watan Janairu ne, kungiyar ta baza mambobinta kimanin 30 cikin motoci kan iyakar kasar da Spain, tare da rakiyar jirgi mara matuki da ke sa ido kan iyakar.

Shugabar Jam'iyyar Masu Tsattsauran Ra’ayi a Faransa, Marine Le Pen, ta soki matakin gwamnati na Shirin rusa kungiyar, tana mai cewa hana fadin albarkacin baki ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.