Isa ga babban shafi
Amurka - Turai

EU da Amurka sun cimma matsaya wajen janye harajin dake tsakani su

Washington da Brussels sun yaba da dama da suka samu ta maido da dankon zumuncinsu, yayin da shugaban Amurka Joe Biden da shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen suka dakatar da haraji kan batun dadden rikicin tallafin kamfanonin jirgin saman kasashensu Airbus da Boing.

Jirgin saman kamfanin Airbus A380, dauke da tutar Boeing a Bourget, ranar  15 watan Yuni sekarar  2015.
Jirgin saman kamfanin Airbus A380, dauke da tutar Boeing a Bourget, ranar 15 watan Yuni sekarar 2015. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Bayan kiran waya da suka yi a ranar Juma'a, Biden da von der Leyen sun sanar da dakatar da harajin kayayyakin dake shigowa kasashen su na biliyoyin daloli har na tsawon watanni hudu, abin da fadar White House ta ce wata dama ce "ta farfado da hadin gwiwar Amurka da EU."

 

 

Yayin da shugabar gudanarwar Tarayyar Turai Von de Leyen ke bayyana farin cikin ta kan sake maido da kyakkyawar alaka tsakanin Amuka da kungiyar.

"Na yi farin cikin yin magana da Shugaba Biden a yammacin yau - na farko da aka yi musayar ra'ayi da kuma fara kyakkyawar alaka," in ji shugaban Hukumar Tarayyar Turai, von der Leyen.

"Ni da Shugaba Biden mun amince da dakatar da duk wani harajin da aka sanya mana dangane da rikice-rikicen Airbus-Boeing, na jiragen sama da na wadanda ba na jirgin sama ba, na farkon har tsawon watanni hudu."

Kiran shi ne na farko da Shugabar Tarayyar Turai ta yi da Biden tun lokacin da ya hau mulki, duk da cewa shugabannin biyu sun tattauna a watan Nuwamba bayan da ya lashe zaben shugabancin Amurka.

Dukkanninsu sun sanyawa juna haraji 

Dukkanin bangarorin sunyi nasara a hukunce-hukuncen da suka shigar gaban Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO kan rikicin wanda ya baiwa gwamnatocin damar sanyawa juna haraji.

Amurka ta lafta wa kasashen tarayyar Turai harajin Dala biliyan 7. 5 sakamakon haramtaccen tallafin kudaden da suke bai wa kamfanin kera jiragen sama samfurin Airbus.

Yayin da Kungiyar Tarayyar Turai ta maida martani wajen lafta wa Amurka harajin da ya kai Dala biliyan 12 kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na bayar da tallafi ga kamfanin jiragen sama na Boeing.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.