Isa ga babban shafi
Turai-Coronavirus

Turai za ta hana fitar da rigakafin Coronavirus daga kasashenta

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula Von der leyen ta yi gargadi kan yiyuwar kasashen kungiyar su dakatar da fitar da alluran rigakafin corona daga Nahiyar dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da tsananta.

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. AP - Aris Oikonomou
Talla

Gargadin na von der Leyen na zuwa ne mako guda bayan Italiya ta hau kujera naki wajen dakatar da aika alluran riga-kafin dubu dari biyu da dari bakwai zuwa kasar Australia, duk da cewa Australian a cewar EU ba ta yanayin bukatar allurar a gaggauce.

Kungiyar ta caccaki kamfanin kasar Sweden da gaza isarwa Turai alluran rigakafin kamar yadda aka tsara maimakon haka sai ya karkatar da su zuwa Birtaniya.

Bisa yarjejeniyar Turai da Kamfanin wajibi ne ya gama wadata ta kasashenta da rigakafin gabanin kaiwa wasu kasashe.

Turai mai yawan jama’a miliyan 446 ko a watan daya gabata sun karbi allurai sama da miliyan 5 zuwa yanzu, yayinda ta ke shirin fara karbar miliyan 10 kowanne wata daga karshen watan Aprilu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.