Isa ga babban shafi
Faransa-Hakkin dan adam

Ministan cikin gidan Faransa ya gurfana a kotu kan zargin fyade

Ministan cikin gidan Faransa  Gerald Darmanin ya bayyana a gaban kotu a yau Juma’a don amsa tambayoyi a karon farko a game da zargin da wata mata ta mai cewa ya yi mata fyade fiye da shekaru 10 da suka wuce, zargin da ya musanta.

Ministan cikin gidan Faransa, Gerald Darmanin.
Ministan cikin gidan Faransa, Gerald Darmanin. THOMAS COEX AFP/File
Talla

Matar mai suna Sophie Patterson-Spatz ta kuma zargi ministan, wanda kusa ne a cikin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron da cin  zarafinta tare da amfani da iko ba bisa ka’ida ba.

Ta ce Darmanin ya yi mata fyade a shekarar 2009  bayan da ta nemi ya taimaka mata wajen soke bayanan aikata laifinta a lokacin da ya ke aiki a matsayin mai bada shawara ga jam’iyar UMP ta fannin shari'a.

An yi watsi da shari’ar a shekarar 2018 bayan da masu gabatar da kara suka ce binciken da aka yi tun da farko ya nuna cewa da yardarta aka yi abin da aka yi, hasali ma babu wani abin da ke nuna cewa an takura mata, ko kuma anyi mata barazana.

Kungiyoyin kare hakkin mata sun harzuka ainun a lokacin da suka ji cewa ba a jima da sake bude shari’ar ba, shugaba Emmanuel Macron ya nada wanda ake zargin ministan harkokin cikin gida.

Darmanin, wanda ya ce da amincewar Patterson-Spatz, ya afka mata, ya mayar da martani ta wajen shigar kara kotu  ta bi masa hakki kan bata masa suna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.