Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Dokar kullen Faransa ta haramta shan barasa

Gwamnatin Faransa ta sanar da shirinta na haramta kwankwadon barasa a wuraren shakatawa, a wani bangare na sabuwar dokar kulle domin takaita yaduwar annobar Covid-19, kamar yadda Firaministan kasar, Jean Castex ya bayyana a yau Alhamis.

Firaministan Faransa Jean Castex
Firaministan Faransa Jean Castex THOMAS COEX AFP
Talla

A yayin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dokokin Faransa, Firaminista Castex ya ce, hukumomin kasar ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tarwatsa taruwar jama’ar da adadinta ya zarce mutun 6 a wuraren shakatawa da suka hada da bakin ruwa da dandalin nishadi a karkashin sabuwar dokar da shugaba Emmanuel Macron ya kaddamar a jiya Laraba.

Castex ya yi tur da mutanen da ke karan tsaya ga sabuwar dokar kullen bayan wasu hotuna sun nuna wani  gungun mutane na holewa da barasa a bakin ruwa da ranar tsaka a wasu biranen kasar da suka hada da Paris da Lyon.

Firaminista Castex ya kara da cewa, ya kamata masu shigar da kara na gwamnatin kasar su tuhumi masu shirya bukuwa a boye saboda yadda suke jefa rayukan jama’a cikin hadari a cewarsa.

Firaministan Faransa na jawabi a zauren Majalisar Dokokin kasar kan sabuwar dokar kulle

Firaministan Faransa na jawabi a zauren Majalisar Dokokin kasar kan sabuwar dokar kulle

A bangare guda, shugaba Macron  ya zartas da dokar rufe makarantu da kuma gudanar da aiki daga gida,  amma ana sa ran zai sassauta matsin lamba kan asibitoci da ke fuskantar karuwar masu fama da coronavirus da suka cika makil a sashin kula da marasa lafiya da ke cikin matsanancin hali.

Kodayake shugaban na Faransa ya ki kafa dokar tilasta wa mutane zaman gida na dole a wannan karo ko kuma hana su walwala baki daya,  yayin da ya amince da tafiye-tafiyen  fasinjoji a lokacin bukukuwan Easter a karshen makon nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.